Yadda Zaka Kirkiri Website Da Wayar Hannunka Ba Tare Da Ka San Code Ba
Gabatarwa
Ka iya kirkirar cikakken website da wayar hannunka kawai, ba tare da ka san code ba, domin AI na rubuta maka code ɗin, kai kuma kana kwafa ka saka shi a intanet kyauta.
A wannan littafi zaka koyi matakai guda uku:
Mataki na ɗaya: Buɗe Gmail, yin rijista da AI, da koyon rubuta prompt da Turanci da Hausa domin AI ya rubuta maka website.
Mataki na biyu: Adana code ɗin, buɗe GitHub, da ƙirƙirar repo.
Mataki na uku: Saka website ɗin a intanet ta Cloudflare Pages ko Netlify, da saita KV.
Abin da kake buƙata
Waya (Android ko iPhone) mai browser kamar Chrome.
Data ko Wi-Fi.
Lambar waya mai aiki, domin karɓar code na tabbatarwa.
Hakuri. Kuskure na farko ba matsala bane, AI zai gyara maka.
Yadda zaka karanta littafin
Ka bi babuka bisa tsari, daga Babi na 1 zuwa na 10. Kowane babi yana da matakai a lamba. Idan wani abu ya bambanta a wayarka, ko kuma kamfani sun canza yanayin shafinsu, ka nuna wa AI hoton abin da ka gani (screenshot) ya yi maka bayani.
Lura: kamfanoni kamar Google, GitHub, Cloudflare da Netlify na canza yanayin shafukansu lokaci zuwa lokaci. Sunayen maɓallai na iya bambanta kaɗan, amma tsarin aikin iri ɗaya ne
Comments